Assalamualaikum warahmatullah. Yan'uwa na barkanku da wannan lokaci yau nazo maku da wani sabon Al'amari Kuma munaso kowa da kowa ya Karu da hakan wannan link din da kuke gani a kasa link din da aka budene domin bin umurnin shugaban kasa na cewa a tallafawa dukkan wani Mai sana'a kanana da manya domin farfadoda tattalin arziki. Inaso kuwa yashiga yadubashi dakyau kafin lokacin Fara ragista yayi.
Ranar Litinin 21 ga wannan watan za'a fara rijistan mutanen dake sana'o'i domin basu tallafin Naira dubu 30,000 wasu kuma Naira dubu 50,000 wanda shugaba Buhari ya ware Naira biliyan Sittin (60 Billion Naira) duba da halin da jama'a ke ciki, domin tallafawa mutane bayan cutar coronavirus ta karya harkokin kasuwancin 'yan kasar.
Ga wanda yake bukatan tallafin, ba bashi bane, sai ya shiga wannan website din ranar da za'a buden ( http://www.survivalfund.ng
) , zaka iya shiga website din kaga yadda gwamnatin ta tsara shirin.